Sarkin Kano ya ziyarci inda aka ta da bom

Image caption Sarki Muhammadu Sanusi ya yi Allah wadai da harin da aka kai Masallacin Juma'a a Kano

A Najeriya, Mai Martaba Sarkin Kano da ke arewacin kasar, Muhammadu Sanusi na Biyu, ya katse aikin Umrah da ya ke yi a Saudiyya, saboda harin da a ka kai babban masallacin birnin ranar Juma'a.

Sarki Sanusi ya ziyarci masallacin da a ka kai harin, da ke kofar gidansa domin duba barnar da a ka yi, daga nan ya koma fadarsa.

Mai Martaba Sarkin wanda ya ba da umarni a tsaftace masallacin, ya ce ba za a taba tsoratar da al'ummar musulmi ba su daina yin addininsu, kamar yadda maharan ke burin gani.

Sarki Sanusi na Biyu ya musanta rade-radin da wasu ke yadawa cewa kiran da ya yi a makon da ya gabata a kan jama'a su tashi su kare kansu daga hare-haren kungiyar Boko Haram ne ya sa a ka kaddamar da harin.

Harin wanda a ka kai lokacin Sallar Juma'a ya yi sanadiyyar mutuwar masallata da yawa da raunata wasu da dama.