Nicolas Sarkozy ya ci zabe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption ''Wannan nasara da na samu a jam'iyya, ta kaddamar da wata sabuwar tafiya ga iyalanmu na siyasa. Inji Mr Sarkozy,

An zabi tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy domin ya jagoranci jamiyyarsa, ta UMP mai ra'ayin 'yan mazan jiya, inda ya yi nasara da kashi 65 cikin dari.

A farkon shekaran nan ne Mr Sarkozy ya sake dawowa fagen siyasar Faransan gadan-gadan, kuma ana ganin matakin nasa na jagorantar jam'iyyar a matsayin shirin sake neman shugabancin kasar a shekara ta 2017.

To amma wannan nasara da ya samu ta kama shugabancin jam'iyyar, ana ganin ba a nan kalubalen yake ba, domin, nasarar alama ce ta gwagwarmayar da ke gabansa, a nan gaba, idan ya nemi sake darewa kujerar shugabancin kasar.

A wannan lokaci, Mr Sarkozy, zai iya fuskantar kalubale daga jam'iyyar tasa duk da wannan goyon baya da ya samu daga cikinta a yanzu.

Ita dai jam'iyyarsa ta UMP mai ra'ayin 'yan mazan jiya ta na fama da rikicin cikin gida da kuma badakalar almundahanar kudade.