Ba mu yadda da zabin Jang ba - 'Yan siyasa

Gwamna Jang na Jihar Plateau Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Gwamna Jang na Jihar Plateau

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya sun ce jijiyoyin wuya na kara tashi dangane da matsayin da aka ce gwamnan jihar, Jonah Jang, ya dauka na gabatar da wani dan siyasa daga zuri'arsa a matsayin wanda zai gaje shi a matsayin gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zabukan dake tafe.

Wannan yunkuri na gwamna dai,na neman rarraba kan jama'ar jihar ta Filato, wadda ke yawan fama da rigingimu.

To sai dai gwamnan ya ce ai ba laifi ba ne idan ya nuna wanda yake so ya gaje shi, ko da kuwa dansa ne na cikinsa, amma hakan ba yana nufin an hana sauran 'yan takara shiga zabe ba ne.

'yan siyasar jihar dai sun ce, kama-karya gwamnan ke neman yi musu, kuma ba za su taba amincewa da haka ba.

Karin bayani