'Yan Boko Haram sun kai hari a Shani

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Shani da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Wasu mazauna garin sun ce 'yan bindigar sun kone ofishin 'yan sanda, sun kuma je gidan sarkin, inda suka sace wata sabuwar mota Hilux.

Sarkin dai ba ya gari a lokacin da suka je gidansan.

Wani mazaunin garin, wanda ya samu tserewa, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa mayakan sun katse hanyoyin sadarwa na garin.

Ya ce sun kuma je gidan-baki na marigayi tsohon sarkin garin, sun kone wasu motoci ukku da ke gidan.

Rahotanni sun ce mayakan sun isa garin ne da misalin karfe takwas na dare a ranar Asabar, inda suka yi ta harbe-harbe da kone-kone.

Wannan dai shi ne karo na biyu da 'yan bindiga suka kai hari a garin Shanin a cikin watanni biyar.

Harin dai ya zo ne kwana biyu bayan mummunan harin da aka kai ma babban masallacin Juma'a na Kano, inda hukumomi suka ce an kashe fiye da mutane 100.

Karin bayani