Yau ce ranar AIDS Ko SIDA ta Duniya

Image caption Wani da ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki

Yau Litinin daya ga watan Disamba, ita ce ranar da Majalisar dinkin duniya ta ware domin yaki da cutar AIDS ko SIDA.

A wannan rana ta kowace shekara ana duba irin kalubale da matsalolin da ake fuskanta a wannan yaki da kuma cigaban da aka samu.

Taken bikin na bana, shi ne, 'Hangen nesa da hada kai domin raba al'umma da cuta mai karya garkuwar jiki'.

A wannan rana hukumar lafiya ta duniya, WHO, za ta fitar da sabbin ka'idojin bayar da magungunan rage kaifin cutar.

Ka'idojin sun hada da shawara ga wadanda suka kamu da cutar, kamar ma'aikatan lafiya da karuwai da wadanda aka yi wa fyade.

A 2013 mutane miliyan 13 ne suka samu magungunan rage kaifin cutar a duniya.

Amma har yanzu akwai mutane da dama da ba sa samun kulawa da magunguna akan cutar.