Ana harbe-harbe a Damaturu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Boko Haram sun tsananta hare-harensu a kwanakin nan a Najeriya

Rahotanni daga jihar Yobe a Najeriya, na cewa ana jin karar harbe-harbe da fashewar bama-bamai a babban birnin jihar, Damataru.

Wasu mazauna birnin sun shaida wa BBC, cewa tun da asubahin ranar Litinin 'yan bindiga suka far wa birnin.

Wasu daliban jami'ar jihar ta Yobe, yankin da 'yan bindigar suka bayyana, sun fantsama daji.

Mazauna birnin da suka boye a gidajensu, sun ce suna jin karan jirgin saman yaki da ke shawagi a birnin.

Babu wata sanarwa ko bayani da suka fito daga bangaren hukumomi kawo yanzu.

Jihar ta Yobe da ke arewa maso gabasahin kasar na daya daga cikin jihohi uku da aka sa wa dokar ta-baci a baya saboda hare-haren 'yan Boko Haram.