Za a sanar da gwarzon dan kwallon BBC

Image caption 'Yan wasa biyar ne ke yin takarar lashe kyautar

A ranar Litinin ne za a sanar da dan wasan da aka zaba a matsayin gwarzon dan kwallon Africa na BBC na shekarar 2014.

Za a yi sanarwar ce da karfe 5:30 na yamma a agogon GMT, watau karfe 6:30 a agogon Najeriya da Nijar a shirin talabijin na BBC Focus on Africa.

'Yan wasan da ke yin takarar lashe kyautar su ne: Yaya Toure da Pierre-Emerick Aubameyang da Yacine Brahimi da Vincent Enyeama da kuma Gervinho.

A yanzu haka dai Yaya Toure, dan kasar Ivory Coast da ke buga wasa a Manchester City ta Ingila ne ke rike da kambun bara na kyautar.

Karin bayani