An rufe shafukan sayar da kayan bogi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Agogunan jabu na daya daga cikin kayayyakin da ake sayarwa ta shafukan

Hukumomin 'yan sanda a kasashen Turai sun rufe hanyoyin intanet na shiga shafukan sayar da kayan amfanin jama'a na bogi 292.

Hukumar 'yan sandan Turai, Europol, ta ce, shafukan suna sayar da kayan kawa da tufafin wasanni da kayan laturoni da magunguna da kuma faya-fayan kida da na fim.

Yanzu duk wanda ya nemi shiga shafukan, sai dai ya ga shafukan da suke fadakar da shi kan laifin satar fasaha.

Sai dai kuma BBC ta ce ta fahimci cewa babu wanda aka kama ya zuwa yanzu dangane da zambar.

Amma kuma wata kafa da ke da kusanci da masu binciken, ta ce da alamu nan gaba kadan za a yi kame.

Hukumar 'yan sanadan ta Turai ta ce, tana son daukar matakin gaggawa akan lamarin domin ganin masu zambar ba su cuci mutane da yawa ba, yayin da bikin Kirsimeti ke matsawowa.

Image caption Darektan hukumar 'yan sandan Turai, Europa, Rob Wainwright

Mukaddadshin darektan cibiyar kare hakkin mallaka ta kasa, Bruce Foucart, cibiyar da ta taimaka wajen rufe shafukan, ya ce masu sayar da kayan bogin suna amfani da lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara don zambatar mutane.

Jami'in, ya ce''mutane na bukatar su kare kansu da iyalansu da kuma bayanansu na kudi daga kungiyoyin mazambatan da ke tafiyar da shafukan na karya''.

Europol ta ce, jumullar irin wadannan shafuka da ta rufe ya zuwa yanzu sun kai 1,829, tun da ta kaddamar da aikin a watan Nuwamba na 2012.

Darektan hukumar 'yan sandan ta Turai, Rob Wainwright, ya ce ''keta haddin hakkin mallaka matsala ce da ke karuwa a tattalin arzikinmu da ke shafar miliyoyin masu yin kaya da masu saye''.