An kai harin bam a kasuwar Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Maiduguri ta sha fama da hare-haren Boko Haram

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno sun ce bama-bamai biyu sun fashe a kasuwar Monday da safiyar nan.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce bama-bamai sun fashe ne a lokacin da mutane ke hada-hada.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai kan adadin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata sakamakon wannan harin.

A makon da ya wuce ma an kai hari a kasuwar Monday din lamarin da ya janyo mutuwar mutane fiye da 70.

Harin na Maiduguri na zuwa ne kwanaki uku bayan da aka kai hari a Masallacin Juma'a a Kano, inda mutane fiye da 100 suka rasu sannan wasu fiye da 200 suka jikkata.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da kaddamar da wadannan hare-haren.