Jihar Difa ta Nijar ta hana zurga zurgar ababuwan hawa da dare

Mahamadou Issoufou, Shugaban Kasar Nijar Hakkin mallakar hoto
Image caption Mahamadou Issoufou, Shugaban Kasar Nijar

Hukumomin jahar Difa a Jamhuriyar Nijar mai iyaka da jahohin Yobe da Borno na Najeriya masu fama da matsalar boko haram,sun kafa dokar takaita zirga zirgar motoci da babura daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe.

Hukumomin sun ce sun dauki wannan mataki ne sakamakon hare haren da yan kungiyar boko haram ke dada kaiwa a wasu garuruwan Najeriya masu iyaka da jahar ta Difa.

Gwamnan jahar ta Difa Malam Yakubu Sumana Gawo, ya ce sun dauki wannan mataki ne, bisa karin maganar nan ta Hausawa, " idan ka ga gemun dan uwanka ya kama da wuta to sanya wa naka wuta."

Gwamnan ya ce sun dauki dukanin matakan da suka dace domin dakile duk wata barazanar tsaro a yankin.