Soji za su iya murkushe Boko Haram - Babangida

Image caption Babangida ya ce soji za su iya magance matsalar Boko Haram

Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Babangida ya ce sojin kasar na da azamar iya murkushe 'yan Boko Haram.

Babangida ya ce idan dai aka bai wa sojojin kayan aikin da ya dace, to za su iya gudanar da ayyukansu.

Ya kara da cewa shawarar da mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya bayar cewa mutane su kare kansu ya yi daidai.

Babangida ya ce a matsayinsa na tsohon shugaban kasa ya fuskanci kalubalen rashin tsaro da dama, kuma kowanne shugaban kasa na da nasa hanyoyin da zai bi domin magance matsalolin.