An kafa dokar hana fita a Damaturu

Harin Boko Haram a Damaturu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harin Boko Haram a Damaturu

Rahotanni daga jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ba dare ba rana a babban birnin jihar Damaturu.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne domin bai wa jami'an tsaro damar zakulo wasu daga cikin maharan da suka boye a birnin bayan harin da suka kai ranar Litinin.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnatin jihar Abdullahi Bego ya sanya wa hannu, gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne domin bai wa jami'an tsaron damar gudanar da wannan aiki da kyau.

Karin bayani