An sassauta dokar hana fita a Damaturu

Hakkin mallakar hoto yobe govt
Image caption Hankali ya soma kwanciya a garin Damaturu

Gwamnatin Jahar Yobe a Najeriya ta bada sanarwar sassauta dokar nana fitar data sanya ta sa'oi 24 a garin Damaturu.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa Gwamnan Jahar shawara na musamman kan harkokin yada labarai Abdullahi Bego, ta ce dokar hana zirga- zirgar za ta soma aiki ne daga ranar Laraba daga karfe 6 na yamma zuwa 7 na safe.

Don haka sanarwar ta ce jama'a a garin na Damaturu na iya gudanar da harkokinsu daga karfe 7 na safe zuwa 6 na yamma kama daga Larabar.

Gwamnatin jahar tace ta dauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro.