Ebola na dakile tattalin arzikin kasashe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jim Yong Kim, ya ce halin da ake ciki ya sa dole a kara tashi tsaye kan cutar

Wani sabon rahoton da bankin duniya ya fitar ranar Talatar nan, ya nuna cewa annobar Ebola tana dakile cigaba da kuma tattalin arzikin kasashen da cutar ta fi kamari.

Rahoton ya nuna cewa hakan zai shafi cigaban kasashen na Guinea da Liberia da kuma Saliyo, a shekara mai zuwa yayin da suke kokarin kawar da cutar.

Alkaluman rahoton sun nuna cewa kasashen uku za su rasa kudin da ya kai sama da dala miliyan dubu biyu daga abin da aka yi hasashe za su samu a 2014 zuwa 2015 a sanadiyyar cutar.

Haka kuma rahoton ya gano cewa tasirin annobar a kan kasafin kudin kasashena ta fi ta sama dala mliyan dari biyar a wannan shekara ta 2014 kadai.

An fitar da wannan rahoto ne yayin da shugaban Bankin duniyar Jim Yong Kim, zai fara ziyarar kwanaki biyu a yankin Afrika ta Yamma, domin duba tasirin annobar ta Ebola.

Haka kuma zai tattauna da gwamnatoci da hukumomi na duniya kan matakan da ya kamata a dauka don kawo karshen cutar cikin hanzari.