'Yan Al Shabaab sun hallaka mutane 36

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption 'Yan Al Shabab ne ke da iko da wurare da dama a Somalia

Mayakan kungiyar Al Shabaab sun ce su ne suka kashe ma'aikatan fasa dutse su talatin da shida a arewa maso gabashin Kenya.

Rahotanni sun ce maharan sun je Mandera ne cikin dare a lokacin da ma'aikatan na barci a cikin tantunansu sannan suka harbe su da bindiga.

Shaidu sun ce sai da aka raba Musulmi da wadanda ba Musulmi ba kafin 'yan Al Shabaab din su kashe su.

Kwanaki goma da suka wuce 'yan Al-Shabaab sun hallaka fasinjoji 28 wadanda ba Musulmi ba lokacin da suka tare motarsu a kusa da kan iyakar kasar da Somalia.

A ranar Litinin ma an kashe mutum daya sannan wasu da dama suka jikkata lokacin da aka kai a hari a wata mashaya a garin Wajir.