Najeriya: 'Yan fansho na barazanar yin zanga zanga

Nigeria
Image caption Zanga zangar tsofaffin ma'aikata ba sabon abu bane a Najeriya

'Yan fansho a jihohin arewa maso gabashin Nijeriya na ci gaba da kokawa kan yadda gwamnatoci suka yi watsi da su dangane da kudadensu na sallama daga aiki da ake kira garatute.

Yanzu haka ma tsofofin ma'aikatan akasarinsu dattawa na barazanar gudanar da zanga-zanga a duk fadin yankin nan da ranar goma sha daya ga wannan wata na Disamba.

A cewar tsofaffin ma'aikatan za su yi zanga zangar ne muddin gwamnatocin jihohin yankin basu yunkura wajen rage basusukan dake kansu ba.

To sai dai kuma hukumomin na cewa suna fama da karancin kudi ne, don haka 'yan fanshon su kara hakuri domin za a biya su nan gaba.