Korea ta haramta daukar hoto da turke

Jami'an tsaron Korea ta Kudu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an tsaron Korea ta Kudu

A Korea ta Kudu tallar turken nan da mutane kan yi amfani da shi don daukar kansu hoto zai iya ja ma mutum tarar fam 17,300 muddin dai ba a yi rajistar na'urar ba.

Hukumar dake tafiyar da hanyoyin sadarwa na Radio sun bullo da wasu dokoki wadanda suka haramta sayar da wannan turke muddin dai ba a yi masa rajista ba.

Dokar tana aiki ne a kan turakun da kan yi amfani da Bluetooth wanda kan yi amfani da naurar da kan zaburar da waya daga wani wuri nesa ta dauki hoto.

Hukumar tace, turakun da ba su da rajista za su iya yin kutse cikin sauran wasu na'urorin dake amfani da irin wannan hanyar ta iska.

Wannan turke na daukar hoto wanda za a iya dora masa wayoyin salula na zamani don daukar hoton masu su daga wurinda ya zarce tsawon hannun mutum suna kara yawa kuma na'u'oin da suka fi jan hankali a cikinsu kan yi amfani da fasaha ta zamani ta iska da radio mai gajeren zango kan yi amfani da ita wajen ta da kamera ta waya daga wani wuri nesa.

Saboda suna amfani da Bluetooth ana kallon wannan naura a matsayin wata na'urar sadarwa, shi yasa kuma ake gwada ta da yin rajistar ta da hukumar ta Korea ta Kudu wadda ke sa ido a kan kafofin watsa labarai na Radio kamar yadda wani jami'in hukumar ya shaida ma kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sanarwar da aka bayar a ranar Jumma'a, an yi ta ne da nufin sanar da mutane cewar lallai ne su yi hattara a kan abinda suke sayarwa a cewar jami'in hukumar.

Dokokin da Ofishin ya buga sun nuna cewar za a iya cin tara ko hukuncin zama gidan Yari ga mutanen da suka yi ko kuma sayar da turakun wadanda ba a yi ma rajista ba.

Kakakin hukumar ya ce, mutane da dama masu tallar irin wadannan na'urori wadanda suke jin kila cikin rashin sani suna sayar da naurorin da ba a yi musu rajista ba, sun buga musu waya suna neman karin bayani.

Kawo yanzu dai ba a fara amfani da dokar ba ka'in da na'in, kuma babu wani wanda ke sayar da irin wadannan turaku da aka ba da labarin 'yan sanda sun kame.

Karin bayani