Kamaru: Jam'iyun adawa sun soki kudurin gwamnati

Cameroon Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan adawa sun ce ana so ne a hanasu yin zanga zangar lumana

A Jamhuriyar Kamaru, Jam'iyyun siyasar bangaren 'yan adawa sun soki kudurin dokar zantar da hukuncin kisa akan wanda aka samu da aikata laifin ta'addaci.

Gwamnatin kasar ce dai ta shigar da wannan kuduri a gaban majalisa domin ta nazarta.

Baya ga ta'addaci kuma kudurin ya yi bayani akan tada bore wanda ka iya cin zarafin jama'a da kuma yin barazana ga madafun iko, ko kuma neman jama'a da su bijere wa Hukumomi.

Sai dai jam'iyyar MRC ta yi zargin cewa duk wadannan dabaru ne na gwamnati na yin barazana domin kada abinda ya auku a kasar Burkina-Faso inda jama'a suka tilasatawa shugaban kasa sauka daga kan mulki ya faru Kamaru.