'Akwai 'yan Chadi cikin mayakan Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Boko Haram sun addabi Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi

Daya daga cikin 'yan sintirin da suka taimaka aka kwato garin, Mubi daga hannun Boko Haram ya shaida wa BBC cewa akwai 'yan kasar Chadi da ke yaki tare da Boko Haram.

Umar Dawaki ya ce ya kashe Boko Haram sama da 10, kuma ya fahimci cewar wasunsu 'yan kasar Chadi ne bisa la'akari da tsagen da ke fuskokinsu.

Ya ce "Wadanda na harba da hannu na suna da tsagen 'yan Chadi, basa Hausa irin nawa, suna hadawa da Faransanci."

Makaman da Dawaki ya ke amfani da su sun hada da wuka, kwari da baka da kaho mai dauke da guba.

"Wuka ba za ta ci mu ba, bom ba zai kashe mu ba," in ji Dawaki.

Sakamakon hadin gwiwa tsakanin 'yan sintiri da jami'an tsaro, yanzu haka gwamnatin Nigeria ta yi nasarar kwato garuruwa da dama daga hannun 'yan Boko Haram.