Boko Haram: 'yan sintiri na taka rawar gani

Image caption Umar Madaki ya ce babu gudu babu ja da baya

"Nigeria kasata ce, kuma a shirye nake da na sadaukar da rayuwata domin kasata", in ji Umar Madaki, yana mai zubar da hawaye.

Madaki tshohon mafarauci ne wanda ya kwashe shekaru yana gadin makabarta a garin Yola ta arewa maso gabashin Nigeria, wanda kuma a halin yanzu ya bi sahun 'yan kato da gora domin yakar 'yan kungiyar Boko Haram.

Dan sintirin ya bayyana cewa ko a makon da ya gabata ya bi sojojin Nigeria har kusa da garin Mubi don fafatawa da 'yankungiyar ta Boko Haram.

Dawaki ya ce ya kashe Boko Haram sama da 10, kuma ya fahimci cewar wasunsu 'yan kasar Chadi ne bisa la'akari da tsagen da ke fuskokinsu.

Makaman da Dawaki ya ke amfani da su sun hada da wuka, kwari da baka da kaho mai dauke da guba.

"Wuka ba za ta ci mu ba, bom ba zai kashe mu ba" in ji Dawaki, ya na mai yin nuni ga guru da laya masu dauke da ayoyin alkur'ani da ya ke sanye da su.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sintiri sun shirya shiga daji

Tijjani Muhammad, wani tsohon ma'aikacin gwamnati wanda shi ma bai jima da dawo daga fagen fama ba, ya bayyana cewa kishin al'umma ne ya sa su ke yin wannan aiki, kuma su na mayar da hankali ne a kan hakan yayin da su ka fita fagen fama.

Sai dai kuma ya bayyana cewa an kashe musu mutune uku sannan bakwai sun jikkata, amma duk da hakan ya ce ana samun nasarar yakar 'yan ta'addar.

'Gwamnatin Adamawa ta sa hannu'

Gwamnan jihar Adamawa, Bala Ngilari a hirarsa da BBC ya ce "yanzu mun yi wa 'yan kato da gorar tsari, mun basu dama mun sama musu ababan hawa".

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sintiri sun yi tasiri a Maiduguri

Ngilari ya kara da cewa burinsu shi ne samar da 'yan kato da gora dubu hudu.

Sakamakon hadin gwiwa da rundunar sojojin Nigeria ta yi da 'yan sintiri an samu wanzuwar zaman lafiya a Yola.

Sannan rundunar ta samu nasarar karbe garuruwa da dama na arewacin jihar ta Adamawa da suka hada da Mubi daga hannun mayakan na Boko Haram.