An fara shari'a kan ridda a Pakistan

Image caption 'Yan kasar sun yi zanga-zanga kan wannan batun

'Yan sanda a Pakistan sun fara binciken ridda akan wani tsohon mawaki da ya zama mai da'awar musulunci, bayan kamara ta dauki hotonsa yana kalaman batanci kan daya daga cikin matan Annabi Muhammad SAW.

Junaid Jamshed, wanda daya ne daga cikin jagororin kungiyar 'yan Sunna, ya fitar bidiyon da ya nuna shi yana yin kalaman batancin kan matar Annabi Muhammadu wato Nana Aisha.

Bidiyon dai ya yadu sosai, kuma hakan ya sa wata kungiyar Musulmi 'yan Sunna sun kai kararsa a kotu, suna masu zarginsa da yin ridda.

Jamshed ya sake fitar da wani bidiyon bayan takaddamar ta auku inda ya nemi afuwa.

Ridda ta kasance babban laifi a kasar Pakistan, inda kungiyoyin da ke rajin kare hakkin dan adam ke ganin cewa ana hukunta talakawa da marasa gatan da suka yi riddan ne kadai.