Tsaro: Ana taron wayar da kai a Kano

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jihar Kano na fuskantar kalubalen tsaro

A jihar Kano da ke arewacin Nigeria ranar Alhamis ake kammala wani taron wayar da kai na kwanaki biyu kan kula da tsaro da kuma fadakar da jama'a kan yadda za su kare kan su.

Taron, wanda wani kamfanin tsaro mai zaman kansa ya shirya tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sanda, ya na horar da jami'an gwamnati da hukumomi masu zaman kan su ne, da kuma 'yan kasuwa.

Birnin na Kano dai na kara fuskantar matsalolin tsaro a 'yan kwanakin nan, inda a ranar Juma'a da ta gabata, aka kai hari mafi muni a babban masallacin juma'ar birnin, wanda ya yi asarar rayuka da dama.

Harin na ranar jumu'a dai ya sa mutane yin azumi tare da gudanar da addu'oi bayan kiran da Sarkin Kanon ya yi musu.