An kai hari a garin Bajoga na Gombe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A kwanakin baya ma mutanen da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kamfanin yin siminta na Ashaka da ke jihar ta Gombe

Mazauna garin Bajoga na jihar Gombe da ke Najeriya sun ce wasu mutane sun kai hari a garin da safiyar ranar Alhamis.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan girman harin.

Sai dai mazauna garin na zargin cewa maharan 'yan kungiyar Boko Haram ne.

A watan jiya ma maharan sun kai farmaki a masana'antar siminti ta Ashaka da ke jihar ta Gombe, kuma sun yi awon-gaba da nakiyoyin da ake fasa duwatsu da su.

Jihar Gombe na da sansanonin 'yan gudun hijirar Boko Haram da dama.