Kura ta lafa a Bajoga, Gombe

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga garin Bajoga na jihar Gombe sun ce kura ta lafa bayan da wasu mahara da ake zargin 'yan kungiyar boko Haram ne suka kai hari kan garin Bajoga da safiyar jiya inda suka kona ofishin 'yan sandan garin.

Mazauna garin dai sun ce sun ji karar harbe-harbe da fashewar abubuwa, lamarin da ya sa dubban jama'a gudun tsira da rayukansu a ranar Alhamis da safe.

Sai dai wani mazaunin garin ya shaidawa BBC a ranar Alhamis da daddare cewa 'kowa ya shiga gida yanzu haka, kuma ba motsin kowa, garin ya yi shiru'.