'Hukuncin kisa kan 'yan Boko Haram a Kamaru'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru na jiran 'yan Boko Haram

Jam'iyyun siyasar bangaren 'yan adawa a jamhuriyar Kamaru sun soki kudurin dokar zartar da hukuncin kisa a kan wanda aka samu da aikata laifin ta'addanci.

Gwamnatin Shugaba Paul Biya ce ta shigar da kudurin a gaban majalisa domin ta nazarta.

Baya ga ta'addanci kuma, kudurin ya yi bayani a kan tada-bore wanda ka iya cin zarafin jama'a da kuma yin barazana ga madafun iko, ko kuma neman jama'a da su bijere wa hukumomi.

Sai dai jam'iyyar MRC ta yi zargin cewa duk wadannan dabaru ne na gwamnati na gudun kada abinda ya auku a kasar Burkina-Faso ya faru, inda jama'a suka tilasatawa shugaban kasar sauka daga kan mulki.

Kasar Kamaru na daga cikin kasashen da 'yan Boko Haram ke kai wa hare-hare.