Daruruwan mutane sun yi gangami a New York

US Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu gangamin suna so ne a yi adalci

Daruruwan mutane sun yi gangami a birnin New York domin su nuna rashin jin dadinsu kan matsayar da mahukunta suka dauka na cewa ba za a tuhumi wani dan sanda farar fata da ya kashe wani mutum bakar fata ba.

Masu zanga zanga sun taru ne a dandalin Foley Square kusa da Shelkwatar 'yan sanda, suna kira da a yi adalci.

Shi dai dan sandan ya kashe bakar fatar mai suna Eric Garner ne wanda baya -dauke -da -makami, bayan da ya makure shi, lamarin da ya sa numfashin Mr Garner ya dauke.

A wani taron manema labarai, Magajin Garin New York, Bill de Blasio ya ce ya kamata a kyautata dangantakar dake tsakanin 'yan sanda da al'umomi.

Sannan ya kara da cewa akwai bukatar mutane su gane cewa ran baka fata na da muhimmanci daidai da na farar fata.

Rahotanni sun ce an yi zanga zangar ma a wasu biranen Amurka yayin da 'yan sanda suka facek mutane 83 a birnin New York.