Amurka: An kaddamar da binciken kan kashe bakar fata

US Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a gudanar da binciken ne a karkashin gwamnatin tarayyar kasar Amurka

Babban Attorney Janar din kasar Amurka Eric Holder, ya kaddamar da bincike kan kisan da wani dan sanda farar fata ya yiwa wani bakar fata.

Dan sanda ya kashe bakar fatar ne a birnin Newv York bayan da ya danne shi yayin da shi bakar fatar ba ya dauke da makami, lamarin da ya sa numfashinsa ya dauke.

Rundunar 'yan sandar New York ta haramta irin wannan tsari na danne wadanda ake zargi da aikata laifi yayin da ake so a kama su.

A baya Lauyan da yake wakiltar iyalan bakar fatar da aka kashe, ya ce ya yi mamaki matuka kan yadda mai taimakawa alkali wajen yanke hukunci ya yi watsi da hujjojin da hotunan bidiyo suka nuna lokacin da dan sandan ya danne Eric Garner, wanda ke fama da matsalar daukewar numfashi ko kuma cutar Asma.

Yanzu haka Magajin Garin New York Bill de Blasio ya yi kira da kada a tada hankula ya yi da babban limamin nan Al Sharpton ya yi kira da a gudanar da wani gangami a mako mai zuwa.