Zabe: 'Yan gudun hijira a Kaduna na nuna shakku

Image caption Yayinda zabe ke tafe, ana kara nuna damuwa kan tsaro

A Jahar Kaduna, a yayin da hukumar zabe ta kasar ke shirin fara raba katunan dundundun na zabe, wasu 'yan jahar musamman wadanda ke gudun hijira a wasu sassa na jahar na ganin kila a ranar zabe sai dai su yi kallo.

Tun bayan zaben shekarar 2011 ne dai wasu musamman a kudancin jahar suka bar garuruwan da suka yi rajista, a yanzu kuma suke tsugunne a wasu garuruwa da ma wasu jihohi.

Ire iren wadannan 'yan gudun hijira sun yi kira da a samar musu da sabbin rumfunan zabe a inda suke a yanzu.

To sai dai hukumar zabe ta kasa na cewa akwai mafita ga 'yan gudun hijirar.

Mr Nick Dazan, jami'in hukumar zabe kan harkokin yada labarai ya ce idan har irin wadannan mutane basu koma garuruwansu na ainihi ba har lokacin zabe, to kuwa za a ba su damar kada kuri'unsu a duk inda suke, matukar suka rubuta wasika a garin da suke gudun hijirar zuwa kwamishinan zabe ta hannun jami'an hukumar.