APC: Tambuwal, El-Rufai sun yi nasara

Image caption Wakilan APC sun zabi 'yan takarar gwamna

Wakilan jam'iyyar APC a Najeriya na jihohi da dama sun zabi mutanen da za su yi takarar gwamnoni a karkashin jam'iyyar shekarar 2015.

A cikin mutanen da aka zaba akwai kakakin majaliasar wakilan kasar, Aminu Waziri Tambuwal a jihar Sokoto da Malam Nasiru El-Rufai a jihar Kaduna da Sanata Amina Alhassan a jihar Taraba.

Sai kuma mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnonin da ke son yin wa'adi na biyu a karkashin jam'iyyar ma dai sun samu tikitin yin hakan.

Gwamnonin su ne: Tanko Almakura daga jihar Nasarawa da Abdulaziz Yari na Zamfara da Ibikunle Amosun na Ogun da Albulfatah Ahmed na Kwara.

Sauran su ne Ibrahim Geidma na Yobe da Abiola Ajimobi na Oyo.