Tsoffin baturan Kwamfuta na samar da hasken wuta

Image caption Hnayar amfani da tsofaffin baturan kwamfuta wajen samar da hasken wuta za ta saukakawa marasa karfi

An gudanar da bincike da tsofaffin batura sannan aka gano cewa kashi 70% na da karfin da zasu iya samar da haske na fiye da sa'oi 4 a rana a shekara

Masu binciken sun ce amfani da baturan da aka daina amfani da su ya fi sauki da amfani da hanyoyin samar da wutar lantarkin na zamani.

An gwada wannan hanya a garin Bangalore na kasar India a wannan shekarar

Ana tsammanin kuma masu sayar da kayayyaki a kan titi wadanda basa kan layukan wutar lantarki da kuma gidajen marasa karfi zasu soma amfani da wannan hanya sosai.

Za kuma a tattauna wannan bincike da aka gudanar a wani taro da za a yi a San Jose, California

Masu binciken suna kokarin ganin sun taimakawa mutane kusan miliyan 400 a India da ba sa kan hanyar layin wutar lantarki