An kama jirgi da makamai a Kano

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rohotanni daga jihar Kano a arewacin Najeria na cewa jami'an tsaro sun kama wani jirgin kaya dauke da makamai da ya yada zango filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, dake Kanon.

Cikin abubuwan da aka gano a cikin jirgin har da jirage masu saukar ungulu, da manyan akwatuna cike da makamai.

Jirgin ya taso ne daga Bangui, babban birnin Jamuriyyar Afrika ta tsakiya kuma ya nufi kasar Chadi ne.

Wakilin BBC a Kano ya ce jirgin ya tsaya ne a Kano don ya sha mai, kuma an tsare shi bayan jikin jami'an tsao ya ba su cewa da wata matsala.

Kawo yanzu dai babu bayani a kan tawagar matuka jirgin.