Gaskiya ta yi halinta----- Kenyatta

Hakkin mallakar hoto afp

Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya ce yana jin cewa an wanke shi sannan ya samu kwanciyar hankali, bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta yi watsi da zarge zargen da ake masa na aikata laifuka akan bil adama.

An zarge Mr Kenyatta ne dai da kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zabukan da aka yi shekerar 2007 inda aka kashe 'yan Kenyan sama da dubu daya.

Masu gabatar da karar da farko sun zargi gwamnatin Kenyan da rike wasu mahimman hujjojin da za su yi amfani da su a kotu, kuma suka ce an tsoratarda shaidu ta hanyar musu barazana.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil adama suka soki wannan matsaya da kotun ta ICC ta dauka.