Gwamnonin PDP sun ziyarci Obasanjo

Olusegun Obasanjo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce sun tattauna matsalar tsaro ne da gwamnoni biyar na PDP

A jiya Alhamis ne wasu gwamnonin jam'iyyar PDP guda biyar, Liyel Imoke na jahar Cross River da Sule Lamido na Jigawa, da Babangida Aliyu na Niger, da Godswill Akpabio na Akwa Ibom, da kuma Isah Yuguda na jihar Bauchi, suka dira a garin Abekuta don yin wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Ganawar, wacce aka fara da misalin karfe 12 da rabi na dare a gidan tsohon shugaban da ke garin na Abekuta, ta dauke su kimanin sa'o'i uku.

Jim kadan bayan kammala ganawar sirrin, Obasanjo ya ce gwamnonin sun ziyarace shi ne domin tattauna matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ke addabar kasar.

Da yake magana a kan faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, Obasanjo ya ce lamarin bai firgita shi ba, yana mai kara da cewa ''A lokacin da kasar ke samun rarar kudade ba a tuna cewa lokaci irin wannan na zuwa ba sai yanzu da lokacin ya zo yake kuma tasiri a kanmu, don haka ya zama wajibi mu zama jarumai mu fuskanci wannan kalubale mu kuma yi abin da ya kamata.''

Da yake nasa jawabin, gwamnan Jihar Niger, Babangida Aliyu, ya ce kasancewar Obasanjo uba ne a garesu ya sa suka yi tattaki don zuwa neman mafita ga tarin matsalolin da Nigeria ke fuskanta. Ya kara da cewa lokaci ya yi da 'yan kasar za su ajiye bambance-bambance waje guda don ceto kasarsu daga halin ni-'ya-su.