Jirgin da aka kama a Kano ba namu ba ne - Rasha

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Makeken jirgin yana dauke da tarin makamai

Ofishin jakadancin kasar Rasha da ke Najeriya ya ce makeken jirgin dakon kayan da aka kama da makamai a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano ba na kasar ba ne.

A ranar Asabar ne jami'an tsaro a jihar kanon da ke arewacin Najeriya suka kama jirgin dauke da makamai da ya yada zango filin jirgin saman na Kano.

Cikin abubuwan da aka gano a cikin jirgin har da jirage masu saukar ungulu, da manyan akwatuna cike da makamai.

Jirgin ya taso ne daga Bangui, babban birnin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya kuma ya nufi kasar Chadi ne.

Wakilin BBC a Kano ya ce jirgin ya tsaya ne a Kano don ya sha mai, kuma an tsare shi bayan jikin jami'an tsaro ya ba su cewa da wata matsala.

Kawo yanzu dai babu bayani a kan tawagar matuka jirgin.