'Yan Boko Haram sun sace mata a Lassa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tun a shekarar 2009 kungiyar Boko Haram ke kaddamar da hare-hare a Najeriya

A Najeriya, wasu da ake zargi 'yan Kungiyar Boko Haram ne sun yi awon gaba da wasu mata lokacin da suka kaddamar da hari a garin Lassa da ke jihar Borno.

Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa maharan sun kashe akalla mutane 20, sannan sun kone fiye da rabin gidajen garin.

Mazauna garin suka ce tun a ranar 29 ga watan Nuwamba ne maharan suka fara kaddamar da hari a garin, amma ba suyi nasara ba saboda mutane sun fafata da su.

'Yan kungiyar sun sake komawa garin a ranar Asabar, inda mutanen gari suka sake samun nasara akan su.

A harin da suka kaddamar ranar Laraba, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun yi amfani da manyan makamai da suka hada da tankoki na yaki, inda suka yi galaba a kan mutanen garin.

Tun a shekarar 2009 kungiyar Boko Haram ke kaddamar da hare-hare a Najeriya, inda a halin yanzu ta ke rike da iko da garuruwa da yawa a wasu jihohin arewa maso gabashin kasar.