Aleiro ya sake sauya sheka daga PDP

Image caption Aleiro ya ce shugabannin APC na kasa da gwamnoni sun roke su su zo a yi tafiyar da su

Tsohon gwamnan Jihar Kebbi kuma tsohon ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya sake ficewa daga PDP ya koma APC.

Adamu Aleiro ya bayar da sanarwar sauya shekar ne shi da magoya bayansa daga jam'iyyar mai mulkin Najeriya a karo na biyu a cikin daren Lahadi.

Tsohon gwamnan ya ce sun fice daga jam'iyyar ne saboda abin da ya kira tsabagen rashin adalci, inda hatta katin shedar zama dan jam'iyya aka hana su tun shigarsu PDP, da kuma hana mutanensa takara.

Game da samun takara a APC, Adamu Aleiro ya ce ai ba su makara ba domin jam'iyyar APC a cewarsa ba ta nuna bambanci tsakanin duk wanda shige ta.

A martanin da ta mayar PDPn ta bakin kakakinta na jihar Kebbi,Ibrahim Umar Ummai, ta musanta zargin rashin adalcin da Aleiron ya yi na hana mutanensa takara.