Shugaban Malawi ya hakura da karin albashi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Mutharika ya ce sai tattalin arzikin Malawi ya habbaka zai amince da karin albashinsa

Shugaban kasar Malawi, Peter Mutharika da mataimakinsa sun fasa wani yunkuri na kara wa kansu albashi, wanda ya janyo ce-ce-ku-ce.

Mista Mutharika da mataimakinsa, Saulos Chilima, su ka ce ba za su amince da karin albashin nasu ba har sai tattalin arzikin kasar ya habbaka.

Sai dai mawuyaci ne hakan ya yiwu.

Tattalin arzikin Malawin dai ya na cikin mawuyacin yanayi, tun bayan da kasashen yammaci suka dakatar da tallafin dala miliyan 150 da suke bai wa kasar, sakamakon wata badakalar rashawa da ta janyo faduwar tsohuwar gwamnatin kasar.

A lokacin badakalar ta Cashgate, an samu wasu jami'an gwamnati da suka boye makudan kudade a karkashin gadajensu, da cikin motocinsu.

Har yanzu 'yan majalisar dokokin kasar suna sa rai da karin kashi 300 cikin dari na albashinsu, daga dala 250 da ake biyansu a kowanne wata.