An fara gano gawarwakin dalibai a Mexico

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Iyayen wasu daga cikin dalibai 43 da suka bace a Mexico

Jami'an Mexico sun ce an gano akalla gawar daya daga cikin dalibai 43 da suka bace sama da watanni biyu, a wani wurin zubar da shara a jihar kudu maso yamma ta Guerrero.

Wani daga cikin dangin dalibin, Alexander Mora, ya kuma sanya sako a wani shafin sada zumunta na intanet cewa masu binciken kwakwaf sun gano cewa kashinsa ya yi daidai da na kwayar halittar gawar dalibin.

Masu gabatar da kara sun ce jami'ai ne suka dankawa wani gungun 'yan daba daliban su kuma suka kashe su, bayan da wata zanga zanga kan wariyar da ake nunawa wajen daukar aiki ta rikide ta zama tarzoma a garin Iguala.

Batan daliban da ke koyon aikin malanta ya haifar da zanga-zanga tsawon makwanni akan rashawa da tashe tashen hankali a Mexico.