Tsoffin baturan kwamfuta na iya samar da lantarki

Hakkin mallakar hoto IBM
Image caption Kusan mutane miliyan 400 ba sa samun lantarki ta hukuma, sukan dogara da wasu hanyoyi na kansu

Tsofaffin baturan kwamfutar tafi da gidanka suna da karfin da za su iya samar da hasken lantarki a gidajen talakawa.

Wani bincike da masana na kamfanin IBM suka gudanar a India ne ya tabbatar da haka.

Kwararrun sun gano cewa tsoffin baturan suna da karfin kashi 70 cikin dari da za su iya samar da hasken tsawon sama da sa'oi hudu a rana har tsawon shekara daya.

Masu binciken sun ce, amfani da tsofaffin baturan ya fi sauki akan amfani da sauran hanyoyin samun lantarki.

Kuma hakan zai iya taimaka wa wajen rage yawan sharar kayan kwamfuta.

A wannan shekarar ne aka jarraba wannan bincike a birnin Bangalore a shekaran nan.

Ana ganin wannan bincike zai sa masu kasa kaya a titi da talakawa da ba sa kan manyan hanyoyin samun lantarki su rika amfani da baturan.

Hakkin mallakar hoto IBM
Image caption Na'urar Ur Jar da ke sarrafa wutar tsohon batirin karamar kwamfuta (Laptop) don samar da haske

Kwararrun sun kirkiro wata na'ura da suka kira Ur Jar da suke hada ta da tsoffin baturan ta samar da haske da sarrafa msu na'urori marassa jan wuta sosai.

Kwararrun na neman taimaka wa mutane kusan miliyan 400 da ba su da wutar lantarki a India ta wannan hanya.

Masu binciken kamfanin na IBM, sun ce ana zubar da kwamfutoci 142,000 kullum a Amurka, kusam miliyan 50 a shekara.

Ita ma India, wadda kasuwarta ta kwamfuta ke bunkasa tana samar da sharar kayayyakin kwamfutar kusan tan 32 a duk rana.