Faransa ta ce makaman ta ne a jirgin Kano

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Makeken jirgin yana dauke da tarin makamai

Faransa ta ce makaman da aka kama a wani jirgin saman Rasha a Kano nata ne.

Wani kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya a Bangui, babban birnin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ya shaidawa BBC cewa makaman na dakarun kasar ne dake Chadi.

Tun farko Rasha ta ce jirgin da aka tsare a Najeriya da makamai a Kano nata ne, duk da cewa a baya ta musanta.

Kakakin ofishin jakadancin Rasha a Najeria, Artem Romanov ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labaran TASS.

Mista Romanov ya ce "Jirgin da aka tsare a Kano namu ne, sai dai makaman na dakarun wanzar da zaman lafiyar Faransa ne."

Sai dai kuma tun farko ofishin jakadancin ya ce jirgin ba na Rasha ba ne.

A jiya ne aka tsare makeken jirgin dauke da jirage masu saukar ungulu biyu, da motocin soji da bingogi da albarusai da sauran makamai.

Har yanzu dai ana cigaba da tsare jirgin da matukansa.

Hukumomin Najeriya dai ba su ce komai ba dangane da jirgin.

A daren Asabar ne jirgin ya yi saukar gaggawa a Kano a kan hanyarsa ta zuwa kasar Chadi.

Kuma rohotanni sun ce jami'an tsaro a filin jirgin saman Kanon, sun bukaci su gudanar da binciken kwakwab ne a kan sa ganin ba su gamsu da yadda kwatsam ya sauka da tsakar dare ba.

Lamarin dai ya sa tsoro a zukatan mazauna Kanon da sauran sassan Najeria.

Kasar dai tana fama da rikicin Boko Haram da ya haddasa asarar rayuka da dama.

Kuma har yanzu kungiyar na cigaba da tsare 'yan matan Chibok sama da dari biyu da kuma yankuna masu yawa a arewacin kasar.

Karin bayani