Makaman mu ne a cikin Jirgin nan - Faransa

Jirgin Sama Hakkin mallakar hoto NASA
Image caption Jirgin Sama

Kasar Faransa ta amsa cewa makaman da ke cikin jirgin nan da aka kama a Kano nata ne.

Wata kafar gwamnatin faransan ta ce makaman za a yi amfani da su ne wajen aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Chadi.

A jiya ne dai ofishin Jakadancin Rasha a Najeriya ya amsa cewa jirgin mallakar kasar Rasha ne bayan da farko ya musant hakan.

Kame jirgin dai ya janyo doguwar muhawara a kafofin watsa labaran kasar ta Nijeriya ganin fadar da aka yi cewa mayakan Boko Haram wadanda suka jima suna kai hare-hare a arewacin Nijeriyar, suna da daurin gindi na kasashen waje.

Karin bayani