'Yan siyasar Nigeria na bukatar gwajin kwakwalwa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Likitocin sun ce 'yan siyasar Najeriya na yin kalaman tayar da fitina

Kungiyar likitoci ta Najeriya ta bukaci a yi gwajin kwakwalwar 'yan siyasar kasar da ke son yin shugabanci a zaben 2015 domin a tantance yanayin hankalinsu.

A wata sanarwa da kungiyar likitocin ta fitar bayan wani taro da ta kammala a birnin Jos na jihar Plateau, ta ce ya kamata hukumar zaben kasar ta bai wa likitocin damar yi wa 'yan siyasar gwajin.

Shugaban kungiyar Dr Kayode Obembe, wanda ya karanta sanarwar, ya ce akwai bukatar yin gwajin ganin yadda 'yan siyasa ke yin kalamai na tayar da hankali gabanin babban zaben kasar.

Ya kara da cewa bai kamata a fuskanci wata sabuwar matsala a kasar ba, domin kuwa kasar tana fama da matsalolin rashin tsaro musamman na hare-haren 'yan Boko Haram