Korea ta Arewa - Bani da hannu a kutsen Sony

Jagoran Korea ta Arewa Hakkin mallakar hoto
Image caption Jagoran Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta musanta yin kutse a matattarar bayanai ta Sony, to amma kwararru suna tababa.

Wani jami'in diplomasiyya na Korea ta Arewa a birnin New York ya ce kasar sa ba ta da hannu a harin da aka kai ma matattarar hotuna na kamfanin Sony a cewar rahotanni.

Wasu mutane sun samu bayanan sirri na kamfanin bayan kutsen da aka yi a matattarar bayanansa a watan da ya gabata.

Gidan radiyo na Muryar Amurka ya ruwaito jami'in diplomasiyyar da ba a bayyana sunan sa ba yana cewar ikirarin da aka yi cewar Korear ta Arewa ce ke da alhakin wannan kutse, karya ce kawai aka kitsa.

Kamfanin na Sony ya yi hayar wasu kwararru da za sau yi masa bincike, amma dai ba su rigaya suka bayyana tushen harin ba.

Wasu masu bincike masu zaman kansu sun ce akwai kwararan shaidu da suka nuna cewa, harin da aka kai ma matattarar bayanai ta internet ya samo asali ne daga kasar ta Korea ta Arewa.

Kamfanin Sony ya dauki hayar kamfanin FireEye na wasu kwararru masana harkokin tsaro don su bincika wannan kuutse, wanda aka ba da rahoton ya sanya komputoci da dama na Sony suka daina aikin da ya kamata su yi, har ma aka shaida ma ma'aikatan kamfanin su kashe su.

Cikin masu binciken har da hukumar bincike ta tarayya a Amurka FBI - hukumar ta shaida ma kamfanoni cewar su sa ido sosai ga tsutsar Komputar da aka gano a baya-bayan nan.

Shafin watsa labarai na ayyukan fasaha Recode a ranar laraba ya ce babu makawa kamfanin na Sony da FireEye za su bayar da sanarwa cewar Korea ta Arewa ce ke da alhakin tura tsutsa komputar - kodayake tuni kamfanonin suka musanta wannan.

Sai dai kuma masu bincike masu zaman kansu kamar kamfanin Trend Micro sun yi nunin kamannun dake akwai na yanayin tsutsar komputar da aka turo wadda ta shafi shafin na kamfanin Sony da wata wadda aka tura ma Korea ta Kudu a bara.

Gwamnatin Korea ta Kudu ta ce wannan hari da aka yi ma lakani da Dark Seoul - Korea ta Arewa ce ke da alhakin kai shi - sai dai kuma kamar sauran hare-haren da ake kaima shafukka na internet, ba a taba tabbatar da tushen sa ba.

Karin bayani