An yi kutse a shafin wasan kwanfuta na Sony

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu kutsen, Lizard Squad, sun ce za su yi aika-aika a shafukan intanet a lokacin kirsimeti

Wasu masu kutse a shafukan intanet sun dauki alhakin kai hari a shafin wasan kwamfuta(PlayStation) na Sony.

Wannan kutse da 'yan kungiyar mai suna ''Lizard Squad'' suka yi ya sa an daina ganin shafin ranar Litinin.

Masu ziyarar shafin sun rika gamuwa da sakon da ke nuna musu cewa, ''babu shafin! Ba matsalarka ba ce, matsalar intanet ce''.

Wannan shi ne kutse na baya-bayan nan da aka yi wa shahararren kamfanin na Sony.

A watan da ya gabata aka yi kutse a rumbun bayanan dakin hada fina-finai na kanfanin da ke Hollywood.

Daga bisani aka fitar da wasu bayanai na sirri na wasu fina-finai da ba a fitar da su kasuwa ba.

Har kuma da bayanan da suka shafi albashin taurarun fina-finai.

Hakkin mallakar hoto AFP

Kamfanin na Sony ya bayyana cewa yana sane da kutsen da aka yi wa shafin nasa na wasannin kwamfutar.

Ya kuma bai wa jama'a hakuri da cewa yana gudanar da bincike.

Wannan kutse da aka yi wa Sony, ya biyo bayan wanda aka yi wa Microsoft Xbox a makon da ya wuce, lamarin da ya dakatar da shi na akalla kwana daya.

Kungiyar ta masu kutse ta Lizard Squad ta ce ita ke da alhakin wannan kutsen ma.

Masu kutsen sun ce abin da suka yi kadan ne daga wanda zai biyo baya a lokacin bikin Kirsimeti.

Kungiyar masu kutsen dai tana da wani shafin intanet da ke Rasha.