Mai aiki a Uganda ta amsa laifin azabtarwa

Image caption Kotun ya cika makil da 'yan kallo lokacin da aka gurfanadda Jolly Tumuhirwe

Wata mai aiki a Uganda ta bayyana a gaban kotu, inda ta amsa laifin azabtar da karamar yarinyar da aka ba ta raino.

Jolly Tumuhirwe za ta iya fuskantar daurin shekaru 15 a kurkuku idan aka tabbatar da laifinta bayan da aka dauki bidiyonta a asirce.

Bidiyon azabtar da karamar yarinyar ya ta da hankali sosai a duniya.

An nuna mai aikin tana haurin karamar yarinyar kafin ta ja yarinyar a kasa.

An rarraba bidiyon cin zalin sau dubbai a shafukan zumunta na zamani tare da Allahwadai da abinda mai aikin ta yi.