Mai aiki ta amsa azabtar da yarinya a Uganda

Hakkin mallakar hoto Daily Monitor
Image caption Faifan bidiyon ya yadu kamar wutar daji a dandalin sada zumunta

Wata mai aikin gida a kasar Uganda ta amince cewa ta azabtar da wata karamar yarinyar da take kula da ita.

Matar, Jolly Tumuhirwe, na fuskantar shekaru 15 a gidan kurkuku bisa aikata laifin.

Al'amarin dai ya tayar da hankulan mutane a kasar, bayan faifan bidiyon azabtar da yarinyar da aka dauka a asirce ya bazu.

An dai ga mai aikin tana dukan karamar yarinyar tare da tattakata kafin daga bisani ta fitar da ita daga dakin karbar bakin, kuma da alama ta suma a wannan lokaci.