Majalisar Dinkin Duniya ta mika babban koko

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce za ta rage yawan abincin da take bai wa 'ya gudun hijirar Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta mika kokon bara kamar yadda ta saba duk shekara, sai dai wannan shi ne mafi girma a tarihi, inda ta ke neman fiye da $ 16 biliyan don gudanar da ayyukan agaji a badi.

Fiye da dala biliyan bakwai dai za ta ware su ne ga 'yan gudun hijirar Syria, wadanda rikici ya daidaita.

Yayin da kasashen Afghanistan da Iraqi da Sudan ta Kudu da kuma jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ke cikin kasashen da zata fi bai wa muhimmanci.

Kungiyoyin agaji sun ce dole su yanke ayyukansu saboda dala biliyan 13 da aka yi wa Majalisar alkawari a bana, ba a samu kudaden gaba daya ba.