Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 20

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun na fuskantar matsin lamba saboda 'yan Boko Haram

Dakarun Nigeria da ke aiki a arewa maso gabashin kasar sun kashe 'yan Boko Haram sama da 20 a gumurzu biyu da aka yi a jihohin Adamawa da Bauchi.

Rundunar tsaron Nigeria ta ce an fafata a kusa da Hildi na jihar Adamawa da kuma dazukan Balmo da Lamo da suka hada jihohin Borno da Bauchi da kuma Adamawa.

Rundunar ta ce ta kama makaman 'yan tada kayar baya masu yawa a yayin da aka raunata dakarunta bakwai.

Rundunar ta ce kuma ta gano wasu takardu wadanda bisa dukkan alamu da su ne za a yi amfani wajen kai hare-hare a wasu sassan arewa maso gabashin kasar.

Rundunar tsaron Nigeria ta ce za ta ci gaba da iyaka kokarinta domin murkushe ayyukan 'yan ta'adda.