Majalisar dattawan Amurka ta caccaki CIA

Image caption Jami'an CIA na azabtar da mutane

Wani rahoto na majalisar dattawan Amurka ya yi kakkausar suka kan wasu hanyoyi da hukumar leken asirin Amurka CIA, ke amfani da ita wajen tatsar bayanai.

Rahoton ya ce tsarin tamkar rashin imani ne.

Rahoton ya ce babu wani lokaci da irin wadannan hanyoyin tatsar bayanai, wadanda aka bullo da su bayan hare-haren sha daya ga watan Satumba na 2001, su ka yi amfani wajen sanar da wasu hare-haren ta'addanci da aka shirya kai wa.

An rika hana wadanda ake zargi 'yan ta'adda ne barci har na tsawon sa'o'i dari da tamanin, haka an rika wulakanta su, ana kuma lakada masu duka.

Shugabar kwamitin tsaro ta majalisar dattawan Dianne Feinstein, ta yi suka kan yadda ake amfani da wasu 'yan kwangila wajen azabtar da wadanda ake tsaren da su.