Ebola: Saliyo ta sha gaban Liberia

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Cutar Ebola da ta bulla a yammacin Afrika, ita ce annoba mafi muni da aka taba samu

Kasar Saliyo ta wuce makwabciyarta Liberia wajen yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola, a cewar wasu alkaluma da hukumar lafiya ta duniya ta fitar na baya-bayan nan.

Alkaluman sun ce tun lokacin da aka fara annobar a watan Maris na shekarar 2013, mutane 7,780 ne suka kamu da cutar Ebola a Saliyo, yayin da mutane 7,719 ne suka kamu da cutar a Liberia.

Ita kuwa kasar Guinea inda cutar ta fara bulla, alkaluman sun nuna cewa mutane 2,283 ne suka mutu ta hanyar Ebola.

Sai dai hukumar lafiyar ta ce fiye da rabin mutane fiye da 6,000 da suka mutu a kasar Liberia suke.